Aminu Mai Dawayya Ya Bayyana Yadda Ya Taba Mallakar Motoci Sama da 140 Amma Yanzu Ba Shi da Ko Ɗaya

Aminu Mai Dawayya, ɗaya daga cikin tsoffin mawakan da suka shahara a masana’antar Kannywood tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015, ya bayyana wasu abubuwa masu ban mamaki game da rayuwarsa a harkar fim. A cewarsa, akwai wani lokaci da idan ya tunkaro wajen ɗaukar fina-finai ko wajen da jarumai ke taruwa, sai mutane su fara gudu suna cewa: “Ga ɗan maula ya zo.”
Amin7
Aminu Mai Dawayya ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Radiyon Faransa (RFI). Ya ce babu wani jarumi a Kudancin Najeriya ko Arewacin Najeriya da ba ɗan maula ba, domin kowa a masana’antar Kannywood ya taɓa karɓar taimako a wani lokaci. Duk da irin dukiyar da ya samu, ya sha fama da talauci. A cewarsa: “Babu mai yi sai Allah. Na yarda da ƙoƙari, kuma na yarda da akasin sa.”
A wata hira da ya taba yi da Hadiza Gabon, Aminu ya bayyana cewa ya taba samun kyautar motoci har guda 75 daga masoyansa. Haka kuma, ya ce ya sayi motoci kusan guda 70 da kuɗinsa. Shi ne farkon mutum a Kannywood da ya fara hawa motar kansa, kuma shi ne na farko da ya fara zuwa Saudiyya domin sauke farali.
Sai dai, a yau, Aminu Mai Dawayya ya ce baya da mota ko ɗaya. Wannan yana sa wasu su nuna rashin yarda da maganarsa. Amma ya jaddada cewa, da sun san irin martabarsa a shekarun baya, da ba su yi irin wannan tunani ba, ko da wasa.
Ya kuma yi kira ga matasan mawaka da jarumai masu tasowa a Kannywood da su yi amfani da lokacin da suke cikin farin jini wajen gina makomarsu. Ya gargade su da kada su ɓata wannan dama wajen sharholiyar rayuwa da bin abin duniya kawai.