KannyWood

Jarumar Kannywood, Maryam Malika, Ta Roki Kotun Shari’a Ta Tabbatar Da Sakin Da Tsohon Mijinta, Umar, Ya Yi

Jarumar Kannywood, Maryam Malika, Ta Roki Kotu Ta Tabbatar da Sakin da Tsohon Mijinta Ya Yi

Kaduna – Jarumar Kannywood, Maryam Muhammad, da aka fi sani da Maryam Malika, ta shigar da kara a kotun Shari’a da ke Magajin Gari, Kaduna, tana rokon kotun da ta tabbatar da sakin da tsohon mijinta, Umar, ya yi tun shekaru biyar da suka gabata.

Lauyan jarumar, A.S Ibrahim, ya bayyana wa kotu cewa tsohon mijin Malika ya yi mata furucin saki na uku bayan ta nemi saki ta hanyar Khul’i.

Me Ya Sa Malika Ta Kai Kara?

Lauyan ya kara da cewa:

“Ya yi furucin saki sau biyu bayan ta kai kara kotu tana neman saki ta hanyar Khul’i. Daga baya, an kai masa sammaci daga kotu, sai ya rubuta furucin saki na uku a jikin takardar isarwar.”

Bayan wannan furuci na karshe, Malika ta ci gaba da rayuwarta ba tare da komawa kotu ba.

Kotun Ta Dage Shari’a

A zaman kotun na ranar Laraba, 12 ga Janairu, 2025, tsohon mijin Malika bai halarta ba kuma bai turo wakili ba. Alkalin kotun, Kabir Muhammad, ya tambayi mai isar da sammaci ko an kai wa wanda ake kara takardar gayyata, sai dai an tabbatar da cewa ba a same shi a gida ba.

Saboda haka, alkalin ya umarci a ci gaba da kokarin isar da sammaci ta wata hanya, sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 27 ga Fabrairun 2025.

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button